![]() |
|
2020-05-18 21:40:57 cri |
Da yammacin ranar 18 ga watan Mayu bisa agogon Beijing, shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin taro na 73, na taron wakilan dandalin kula da lafiya karkashin hukumar WHO. Ma Zhaoxu ya ce shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawara, game da raba dabaru a fannin kandagarki da shawo kan cutar, hakan ya ma wuce kwarewar da Sin ta samu kawai, domin kuwa matakin ya dace da zahirin yunkuri da ake yi na yaki da cutar a sassan duniya daban daban, yana kuma samar da sabbin dabaru ga wasu kasashe na tsara ayyukan kandagarki, da na shawo kan kalubalen tattalin arziki da ci gaban bil Adama.
A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping, ya jaddada cewa, tallafawa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, wajen gina shinge mai karfi, muhimmin mataki ne a yakin da kasa da kasa ke yi da wannan annoba, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su fadada goyon bayan siyasa, da samar da kudaden gudanarwa ga WHO. Ma ya ce wannan kira ya yi daidai da muhimmancin da ake dorawa kan kasashen Afirka, da goyon baya ga MDD da hukumar WHO, matakin da zai yi tasiri ga yukurin kasa da kasa, na tattara albarkatu don cimma nasarar yaki da wannan annoba. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China