Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa WHO don jagorantar aikin yaki da COVID-19
2020-05-21 11:22:47        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana kudurin kasarsa na yin aiki tare da kasar Myanmar da ma sauran kasashe, don ci gaba da taimakawa hukumar lafiya ta duniya, ta yadda za ta jagoranci aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Xi ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Myanmar U Win Myint. Ya kuma yi kira da a kara zage damtse wajen nuna daidaito da sanin ya kamata a harkokin duniya da martaba dokokin alakar kasa da kasa, da hada kai wajen ganin bayan matsalar kiwon lafiyar al'ummar duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China