Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana adawa da yadda ake illata hadin gwiwar kasashen duniya kan yaki da COVID-19
2020-05-21 11:11:45        cri
Shugaba kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da duk wani yunkuri na illata hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19, da kokarin duniya musamman kasashe masu tasowa na yaki da wannan annoba.

Xi wanda ya bayyana haka yayin zantawa ta wayar tarho da firaministar kasar Bangladash Sheikh Hasina, ya kara da cewa, a shirye kasar Sin ta ke ta ci gaba da aiki da kasashen duniya, ciki har da kasar Bangladash, don taimakawa hukumar lafiya ta duniya wajen jagoranta, da karfafa hadin kan kasa da kasa kan yadda za a hada kai don kandagarki da hana yaduwar annoba, da ma kare lafiyar al'ummar duniya.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, a yayin da kasar Sin ke tsaka da yaki da COVID-19, sassa daban-daban na kasar Bangladash sun taimakawa kasar Sin ta fannoni daban-daban, abin da ke nuna zumuncin abokanta da jama'ar Bangladash suka nunawa Sinawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China