Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi muhimmin bayani kan batun fitar da kabilar Maonan daga kangin talauci
2020-05-20 15:59:57        cri
Kwanan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi muhimmin bayani kan batun fitar da daukacin 'yan kabilar Maonan daga cikin talauci, inda ya ce, yana farin-ciki sosai da ganin yadda rayuwar 'yan kabilar ya kyautata, kuma ba za'a bar duk wata kabila a baya ba a yayin da kasar Sin take kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni. A 'yan shekarun nan, akwai kananan kabilu da dama wadanda suka fita daga cikin talauci, al'amarin da ya kasance wani babban ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kawar da fatara. Shugaba Xi yana fatan 'yan kabilar Maonan za su ci gaba da himmatuwa domin kirkiro sabon rayuwa a nan gaba.

Maonan, na daya daga cikin kananan kabilu 28 a kasar Sin, wadanda ke da mutane 'yan kalilan. Kuma gundumar Huanjiang dake jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai na daya daga cikin gundumomin da ake kokarin tallafawa yaki da talauci. A kwanan baya, wakilan 'yan kabilar Maonan dake gundumar sun rubutawa shugaba Xi wasika, inda suka bayyana farin-cikinsu kan nasarar da aka samu a yaki da talauci, da babban kudurinsu na ci gaba da raya garinsu a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China