Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci Sudan ta kudu da ta hanzarta aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiyar kasar
2020-05-08 10:39:05        cri
Shugaban tawagar MDD a kasar Sudan ta kudu (UNMISS) David Shearer, ya yi kira ga jagororin kasar, da su kammala ragowar sassan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar ta shekarar 2018 da aka cimma, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar dake gabashin Afirka.

Ya ce, jinkirin kafa gwamnatocin jihohin a kasar, ya sa ba a mutunta doka, ga fadan kabilanci a baya-bayan nan dake karuwa a galibin sassan kasar.

Shearer ya shaidawa manema labarai a Juba, babban birnin kasar cewa, MDD ta damu matuka, kan yadda shirin wanzar da zaman lafiyar kasar ya gamu da cikas, musamman wajen nada gwamnonin jihohi a sassan kasar.

Ya yarda cewa, watakila annobar COVID-19 da ta addabi duniya, tana iya shafar aiwatar da yarjejeniyar, amma ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su martaba yarjejeniyar, kana su nada gwamnonin jihohi, da sake kafa majalisar dokoki, su kuma kammala ragowar shirye-shirye na tsaro, ta yadda za a ciyar da shirin zaman lafiyar kasar gaba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China