Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta tabbatar da manufar rage haraji da kudin da kamfanonin za su biya
2020-05-22 10:26:28        cri

Yau Juma'a gwamnatin kasar Sin ta gabatarwa taron wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC rahoton gwamnati, inda ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da rage haraji da kudin da kamfanonin za su biya da inganta manufofi a mataki-mataki, ta yadda za su dace da tsare-tsaren da kasar ke dauka, da kuma tallafawa kamfanoni samun bunkasuwa cikin mawuyacin hali. Rahoton ya ce, za a rage haraji da kudin da kamfanonin za su biya da yawansa ya zarce kudin Sin RMB triliyan 2.5, da kuma yin iyakacin kokarin taimakawa musamman kanana da matsakaicin kamfanoni da 'yan kasuwa, don su shawo kan mawuyancin halin da ake ciki. A sa'i daya kuma, a sa kaimi ga rage yawan kudin da kamfanonin za su kashe wajen samar da kayayyaki, da karfafa taimakon kudade har ma da sanya bankuna su samar da moriya ga kasuwa ta hanyar da ta dace, don rage kudin da za a kashe wajen tattara kudade. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China