Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF: Fasahohin kasar Sin na yaki da COVID-19 sun samar da babban darasi
2020-05-22 09:25:02        cri

Mai Magana da yawun asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Gerry Rice ya bayyana cewa, kasar Sin, ita ce kasa ta farko a duniya da ta dauki managartan matakai kana ta farko da ta fita daga matsalar cutar COVID-19, a don haka akwai darussa da dama da ragowar kasashen duniya za su iya koya daga gare ta.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai ta kafar bidiyo, ya ce a fili yake cewa, kasar Sin tana daukar kwararan matakai don yaki da wannan annoba. Haka kuma kasar Sin tana samun nasara a sauran fannoni, wadanda ka iya zama abin koyi ga saura, inda ya bada misali da tsarin biyan kudi na zamani, da cinikayya ta yanar gizo, da hade kananan kamfanoni da kasuwanni da masu sayayya da sauransu.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana da muhimmiyar rawar takawa, wajen taimakawa duniya da kasashe matalauta, musamman alkawarin da kasar ta Sin ta yi, wajen taimakawa shirin rukunin kungiyar kasashen G20 na saukaka biyan bashin da ake bin kasashe masu karamin karfi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China