Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in IMF: Tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da farfadowa
2020-04-20 16:11:15        cri

Mataimakin daraktan sashin Asiya-Pacific na IMF ya shedawa manema labarai cewa, yanzu Sin tana kokarin komawa bakin aiki da farfado da samar da kayayyaki, matakin da ya sa ake ganin akwai yiwuwar Sin ta samu farfadowa a watannin Afirlu da Mayu da kuma Yuni. Ya kuma yi hasashe cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da farfadowa a rabin shekara mai zuwa saboda ganin an sassauta matakan kandagarkin cutar COVID 19 da kuma manufofin ba da tallafi da gwamnatin ke dauka. Ya ce, a shekara mai zuwa, Sin za ta samu ci gaba mai armashi, a cewarsa kuma, yanzu Sin na fuskantar kalubalen koman bayan tattalin arziki, saboda ganin akwai yiwuwar sake barkewar cutar, abin da zai tilasta gwamnatin Sin ta dauki matakin kandagarki, a hannu guda na daban kuma, saboda annobar ta kara tsananta a sauran kasashe, duniya za ta samu koma bayan tattalin arziki, abin da zai kawo illa ga tattalin arzikin kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China