Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya bayyana rikicin tattalin arzikin 2020 a matsayin mafi muni
2020-03-24 15:21:30        cri

Babbar daraktar asusun ba da lamini ta duniya IMIF, Kristalina Georgieva, ta sanar a jiya Litinin cewa, akwai yiwuwar gamayyar kasa da kasa su fuskanci matsin tattalin arziki mafi muni a 2020, an yi hasashen rikicin tattalin arzikin zai iya kasancewa mafi muni.

Jami'ar ta IMF ta yi wannan tsokaci ne a taron ministocin kudi da manyan bankunan kasashen G20 a game da matakan dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ta addabi duniya, ko da yake mai yiwuwa ne ana sa ran za'a iya farfadowa a shekarar 2021, kamar yadda asusun na IMF ya sanar.

Georgieva ta ce, muddin ana son kaiwa matakin farfadowar, tilas ne a ba da fifiko game da bunkasa fannonin kiwon lafiya a dukkan sassan duniya baki daya. Matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu zai iya kara tsananta, amma idan aka samu nasarar dakile annobar cikin gaggawa, farfadowar tattalin arzikin ya dogara ne kan nasarar da aka samu na saurin warkewa daga cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China