Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun IMF ya yi kira da samar da dabarun da za su takaita mummunan illar COVID-19
2020-03-10 10:30:24        cri

Babbar masaniyar harkokin tattalin arziki ta asusun ba da lamuni na duniya Gita Gopinath ta ce barkewar cutar numfashi ta COVID-19 zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya, don haka akwai bukatar daukar kwararan dabarun da za su taimakawa tattalin arzikin yayin da ake fuskantar annobar.

Gita Gopinath ta wallafa a shafin sada zumunta cewa, wannan matsalar ta lafiya, za ta yi gagarumin tasiri a kan tattalin arziki, wanda zai kawo tasgaro ga harkar samar da kayayyaki da sayensu, daban da wadanda aka gani a baya. Tana mai cewa matsalolin kasuwanci sun sa an rage sarrafa kayayyaki, wanda ya kai ga rashin samar da kayayyaki. Sannan jan kafar da masu sayayya da 'yan kasuwa ke yi wajen kashe kudi, ya rage bukatar kayayyaki.

Har ila yau, jami'ar ta ce ya kamata a dauki kwararan dabaru, ta yadda za a ci gaba da tabbatar da mu'amala tsakanin tattalin arziki da hada-hadar kudi da ma'aikata da kasuwanci, da masu badawa da karbar rance, da kuma tsakanin masu samar da kayayyaki da masu sayayya, domin harkoki su farfado da zarar an shawo kan annobar.

Da take tsokaci kan faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya a makonnin baya-bayan nan, inda ya kai kasa da kaso 30 na matakin da ya kasance a farkon bana, Gita Gopinath ta ce kasashen da suka dogara kan samun jari daga kasashen ketare, ka iya samun kansu cikin hadari, wanda zai iya bukatar karfafa takardun kudadensu ko daukar matakan gudanar kudi na wucin gadi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China