Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun Lamuni na Duniya: Dabarun kasar Sin sun yi tasiri wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-21 15:37:59        cri
Asusun lamuni na duniya IMF, ya ce yanayin da kasar Sin ta samu kanta kawo yanzu, ya nuna kyawawan dabaru sun yi tasiri a yaki da annobar COVID-19 da shawo kan illolinta, duk da cewa wadannan dabarun sun zo da rashin daidaito dangane da tattalin arziki.

Jami'an IMF sun bayyana a jiya cewa, masu tsara manufofi na kasar Sin, sun yi la'akari da iyalai masu rauni da kuma sabbin hanyoyin taimakawa kananan kamfanoni, misali rangwame kan farashin abubuwan da jama'a ke amfani a yau da kullum da bada rance ta hannun kamfanoni masu amfani da fasahar hada-hadar kudi ta zamani.

Jami'an sun kara da cewa, hukumomi sun kuma yi saurin tsara hanyar saukaka bada rance domin taimakawa wajen gaggauta samar da kayayyakin kiwon lafiya da sauran wasu muhimman ayyuka na tunkarar annobar, wadanda suka taimaka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China