Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya yanke shawarar rage ko kawar da bashi ga kasashe 25
2020-04-14 13:51:02        cri
Shugabar asusun ba da lamuni ta IMF Kristalina Georgieva, ta bayyana a jiya Litinin cewa, kwamitin zartaswa na asusun, ya yanke shawarar ragewa, ko kuma kawar da bashi ga kasashe 25, bisa yarjejeniyar asusun ajiya na amintattu, game da dakile tsananin hadurra, da na aikin ceto wato CCRT, domin ba da taimako ga wadannan kasashe 25 a kokarinsu na yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Cikin wata sanarwar da ta fidda a wannan rana, Kristalina Georgieva ta bayyana cewa, Asusun IMF zai samar da kayayyaki ga mambobinsa mafi fama da talauci, da mafiya karamin karfi, da nufin biyan bashinsu na Asusun IMF cikin watanni shida masu zuwa, ta yadda wadannan kasashe za su iya samar da karin kudade a harkokin gaggawa da ma ayyukan ceto. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China