Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yanayin da ake ciki dangane da COVID-19 a Afrika
2020-05-04 11:16:54        cri
Kasar Afrika ta kudu ta ba da rahoton samun karuwar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, kwanaki biyu bayan sassauta matakan kulle da ya shafe makonni 5.

Wata sanarwa da ministan lafiya na kasar Zweli Mkhize ya fitar, ta ce zuwa jiya Lahadi, jimilar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya kai 6,783, wanda ya karu da 447 daga ranar Asabar.

Ita kuwa ma'aikatar lafiya ta Uganda, gargadi ta yi kan rahotannin kafafen sada zamunta dake ikirarin garkuwar jikin 'yan kasar da na sauran al'ummar Afrika na da karfin yakar cutar, tana mai cewa wadannan jita-jita sun haifar da jan kafa dangane da yaki da cutar.

A Masar kuwa, ma'aikatar lafiya ta tabbatar da samun sabbin mutane 272 da suka kamu da cutar, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu zuwa 6,465.

Sanarwar da kakakin ma'aikatar Khaled Megahed ya fitar, ta ce zuwa jiyan, karin mutane 14 sun mutu, inda adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya kai 429. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China