Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na ci gaba da taimakawa kasashen Afirka yakar cutar COVID-19
2020-04-29 13:34:26        cri

Kawo yanzu akwai mutane sama da dubu 33 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar mashako ta COVID-19 a kasashen Afirka, inda kasar Sin ke ci gaba da kokarin taimakawa nahiyar yaki da wannan annoba ta hanyoyi daban-daban, ciki har da fadakar da jama'arsu kan ilimin dakile cutar, da shirya taron karawa juna sani ta kafar bidiyo. Akwai kuma shugabannin kasashe da na jam'iyyun siyasar Afirka da dama, wadanda suka jinjinawa managartan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, gami da gode mata, saboda agajin da ta baiwa kasashen na Afirka.

Kwanan nan, an shirya taron bidiyo ta kafar intanet kan musanyar ra'ayoyi tsakanin kwararrun likitoci na kasar Sin da na kasashen Afirka da dama, inda suka tattauna kan dabarun kandagarki, gami da shawo kan annobar COVID-19, ciki hadda jami'an gwamnati, da kwararrun likitoci kimanin 200 daga kasashen Najeriya, da Lesotho da Zimbabwe su 22.

A dayan bangaren, shugabannin kasashen Afirka da dama, sun jinjina matukar kokarin da kasar Sin ta yi na tallafawa nahiyar, a fannin yaki da annobar COVID-19, inda a cewarsu, dadadden zumunci gami da hadin-gwiwar dake kasancewa tsakanin Sin da Afirka, zai ci gaba da yaukaka.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya ce, goyon-baya da taimakon da kasar Sin ta bawa kasarsa na hakika ne, kana kasar Sin na wani kokari na ci gaba da samar mata da agaji.

Shi kuma ministan lafiya na Jamhuriyar Benin, Benjamin Hounkpatin ya godewa gwamnatin kasar Sin, inda ya ce, bisa tsayayyen goyon-baya da sahihin tallafin da kasar Sin ta bayar, ko shakka babu kasarsa za ta samu galaba kan yakin da take na kawar da annobar COVID-19.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China