Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar kamaru za ta kara daga matsayin matakanta na yaki da COVID-19
2020-05-07 12:11:34        cri

Ministan kudi na kasar Kamaru Louis Paul Motaze, ya bayyana cewa, kasarsa za ta daga matsayin matakanta na gaggauwa kan yaki da cutar COVID-19. Wannan mataki na zuwa ne, bayan da asusun ba da lamuni na duniya(IMF) ya amincewa ya baiwa kasar rancen gaggawa.

Motaze ya shaidawa taron manema labarai a Yaounde, babban birnin kasar jiya Laraba cewa, rancen da asusun ya amincewa ya baiwa kasar, labari mai dadi, ganin yadda kasar ke fama da COVID-19, da ma matakan da gwamnati ta tsara wadanda duk suke bukatar kudade. Ya ce, za a yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace, musamman wajen samar da kayayyaki a asibitoci, da ma muhimman kayayyaki da ake bukata.

A ranar Litinin din da ta gabata ce, asusun IMF, ya amince ya baiwa kasar Kamaru dala miliyan 226, don taimaka mata biyan bukatunta na gaggawa a fannin yaki da COVID-19.

Alkaluman da cibiyar Africa CDC ta fitar na nuna cewa, ya zuwa yanzu, akwai mutane 2,265 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a kasar ta kamaru, ciki har da mutane 108 da cutar ta halaka, sai kuma mutane 934 da suka warke daga cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China