Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har yanzu Amurka ba ta raba kudaden tallafi na dala biliyan 500 ba domin dakile annobar COVID-19
2020-05-19 17:41:44        cri
Kwamitin musamman dake sa ido kan yadda gwamnatin tarayya ke kokarin dakile annobar numfashi ta COVID-19 na majalisar dokokin kasar Amurka ya bullo da wani rahoto jiya Litinin, inda ya ce, daga cikin asusun kudi na dala biliyan 500 da ma'aikatar kudin kasar ta ware na shirin tallafawa tattalin arziki na dala triliyan 2 da majalisar dokokin kasar ta zartas a watan Maris din bana, dala biliyan 37.5 ne kawai aka raba. A lokacin da kamfanonin kasar da dama suke rage ma'aikatansu da kuma dab da durkushewa, akasarin kudaden tallafi dake cikin dala biliyan 500 har yanzu suna hannun ma'aikatar kudin kasar, ba'a raba su yadda ya kamata ba, al'amarin da ya baiwa al'umma mamaki da bacin rai sosai.

'Yan siyasar Amurka da dama sun suki ma'aikatar kudin kasar. Sanata Elizabeth Warren ta ce, yadda ma'aikatar kudi ke amfani da wadannan kudaden ba zai taimaki kamfanonin kasar ko kadan ba. Shi ma kwamitin sa ido na majalisar dokokin kasar ya yi tambayoyi da dama a cikin rahoton da ya fitar, inda a cewarsa, ta yaya za'a raba rancen kudaden? Yaushe ne ma'aikatar kudi za ta iya bayar da rancen? Amma kawo yanzu ma'aikatar ba ta maida martani ko daya ba kan wannan rahoton.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China