Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Laifin da ake aikatawa ya karu a Amurka da Turai sakamakon tsokacin Trump na kyamar kabilu
2020-05-16 16:17:16        cri
A karshen watan Janairun bana, wani mai wasan ban dariya na Birtaniya, 'dan asalin kasar Sin ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, "Kila Basine daya cikin dubu goma, ya kamu da cutar COVID-19 a Birtaniya, amma kusan daukacinsu sun gamu da cin mutunci sakamakon yaduwar cutar."

A ranar 16 ga watan Maris, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fara kiran kwayar cutar COVID-19 da sunan "kwayar cutar kasar Sin" a shafin Twitter, lamarin da ya sha suka daga duk fannoni daga al'ummun kasa da kasa, musamman ma Sinawa. Amma bai daina zargin kasar Sin ba, duk da cewa, ya san kalmomin "kwayar cutar kasar Sin" za su kara kyamar kabilu da hare-haren da ake kai wa Sinawa da 'yan asalin kasashen Asiya.

Tun bayan ranar 20 ga watan Maris, daga Amurka zuwa kasashen Turai, har a fadin duniya, kyamar kabilu da hare-haren da aka kai wa 'yan asalin kasashen Asiya sun kara karuwa cikin sauri. Misali, wani rahoto da aka wallafa a ranar 27 ga watan Maris ya yi nuni da cewa, adadin kalmomin kyamar kabilu da aka wallafa a kan dandalin sada zumunta ya karu har da kaso 900 bisa dari a cikin watan nan.

Kana hare-haren da aka kai wa 'yan asalin kasashen Asiya su ma sun karu. A kwanakin baya, hukumar 'yan sandan Metropolitan ta birnin London na Birtaniya ta fitar da wasu alkaluma, inda aka bayyana cewa, tsakanin watan Fabrairu zuwa watan Maris, gaba daya adadin hare-haren da aka kai wa mutanen dake da fuskokin 'yan asalin kasashen Asiya ya kai 166, wanda ya karu kan 66 da ya kasance a makamancin lokacin bara.

Kila Trump ne ya jagoranci tayar da kyamar kabilu da hare-hare, amma bisa matsayinsa na shugaban babbar kasa a duniya, tsokacinsa da ba sa bisa turba, za su kawo hasarar rayuka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China