Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta yi bayani kan dakunan gwaje-gwajen halittu da ta kafa a ketare
2020-05-17 17:36:43        cri

Kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa, kasar Amurka ta kafa dakunan gwaje-gwajen halittu da dama a kasashen dake kewayen kasar Sin da kasar Rasha, kuma ba ta yi bayani kan harkokin dake nazari cikin wadannan dakunan gwaje-gwaje ba, lamarin da ya kawo damuwa ga gamayyar kasa da kasa.

Bisa labarin da ma'aikatar kare tsaron kasar Amurka ta fidda, gaba daya kasar ta kafa dakunan gwaje-gwajen halittu guda 15 a kasashen dake kewayen kasar Rasha da kasar Sin. Amma, gwamnatin kasar Rasha ta ce, kasar Amurka ta kafa dakunan gwaje-gwajen cikin sirri a kasashe kawancen Soviet da ma kasashe guda 27 dake kewayensu, a halin yanzu, kasar Amurka tana da dakunan gwaje-gwajen halittu sama da dari 2 cikin kasashen duniya.

Haka kuma, bisa binciken da kafofin watsa labaran kasar Rasha suka yi kan dakunan gwaje-gwajen da kasar Amurka ta kafa a kasashen ketare, an ce, harkokin da aka nazari cikin wadannan dakunan gwaje-gwaje sun shafi yadda za a yada cuta ta dabbobi, kwayar halittar bil Adama, nazari kan halittu ta fuskar burin soja da dai sauransu. Har wasu cutuka masu yaduwa sun taba barkewa a wuraren dakunan gwaje-gwaje.

Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Amurka ta ki yin bayani kan dakunan gwaje-gwajen da ta kafa a kasashen ketare, lamarin da ya kawo damuwa matuka ga al'ummomin wadannan kasashe, da ma kasashen dake kewayensu. Wasu mazauna wurin sun bukaci a rufe dakunan gwaje-gwajen kasar Amurkan. Shi ya sa, muna fatan kasar Amurka za ta iya gane bukatun gamayyar kasa da kasa da kuma maida hankali kan kare tsaron al'ummomin wuraren da abin ya shafa, domin daukar matakan da za su dace a kwantar da hankulan al'umma. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China