Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump yana maida siyasa a gaban kome
2020-05-19 17:40:01        cri
Yakin neman zabe da Donald Trump ya yi a shekara ta 2016 ya baiwa mutane da dama mamaki sosai, saboda ganin yadda yake raina kimiyya.

Mutane da dama na ganin cewa, bayan da ya hau ragamar mulkin Amurka, zai sauya ra'ayinsa, kana ba zai yi biris da ra'ayoyin kwararru da darussan kimiyya ba. Amma hakikanin abubuwa sun shaida cewa ba haka yake ba. Duk da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta riga ta sanar da cewa cutar numfashi ta COVID-19 ta zama matsalar lafiya ta gaggawa wadda ta jawo hankalin duk duniya, Trump din bai maida hankali kan illar cutar ba, har bai dauki matakan da suka wajaba cikin lokaci ba.

Bai kamata siyasa da kimiyya su zama doya da manja ba. A yayin da ake kokarin shawo kan wata matsala, masana kimiyya sun yi kokarin nemo shaidu da bullo da dukkan abubuwan da mai yiwuwa za su wakana, ta yadda jami'an gwamnati za su iya yanke shawara a karshe. Amma bai kamata 'yan siyasa su yi biris da ra'ayoyin kwararru ba, har su ki amincewa da daukar alhakin abubuwan da suka faru.

Donald Trump ya dage da yin fatali da dukkan mutanen da suke da ra'ayoyin da suka bambanta da nasa, kuma yana amfani da dukkan fadar White House domin cimma muradunsa a fannin siyasa, abun da zai bata kwarjinin Amurka baki daya. Mene ne dalilin da ya sa Amurka ba ta iya daidaita matsalar yaduwar annobar COVID-19 yadda ya kamata ba? Kila saboda al'adarta ta maida hankali kan batun siyasa maimakon batun kimiyya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China