Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu wadanda suka kamu da annobar COVID-19 a cibiyar tsugunar da bakin haure a Amurka
2020-05-18 13:10:24        cri
Kafar yada labarai ta CBS, ta ruwaito cewa, an samu wadanda suka kamu da annobar COVID-19 a wata cibiyar tsugunar da bakin haure a Amurka.

Hukumar kula da shige da fice ta kasar Amurka ta sanar a ranar 9 ga watan Mayu cewa, cikin bakin haure 2045 daga cikin 27908 da aka yi wa gwajin cutar COVID-19, an samu 986 da suka harbu. Haka zalika wasu jami'an hukumar 44 dake aiki a cibiyoyin tsugunar da bakin huren su ma sun kamu.

Cibiyoyin tsugunar da bakin haure a Amurka na cike da jama'a, lamarin da ya ba cutar saukin yaduwa.

Wasu iyalan wadanda aka tsare sun bayyana cewa, ba a gano cutar da wuri ba, kuma ba a dauki matakan kariya ba, sannan wadanda suka harbu da cutar ba su samu kulawa a kan lokaci ba, kana ba a kebe su ba.

Bakin haure a kalla 149 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a cibiyar Otemesa dake San Deigo, wadda ta kasance cibiya mafi tsanani dake tsugunar da bakin haure a Amurka. A baya-bayan nan ne kwamitin sa ido na majalisar dokokin kasar ta soki hukumar kula da shige da ficen da rashin tunkarar matsalar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China