Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
The Lancet: Gwamnatin Trump ta raunata hukumar CDC ta kasar Amurka
2020-05-17 16:28:47        cri

A jiya Asabar, shahararriyar mujallar ilimin likitanci ta duniya "the Lancet" ta wallafa wani sharhi mai taken "Ya kamata a mayar da iko ga hukumar hana yaduwar cutuka ta kasar Amurka CDC", inda aka soki gwamnatin shugaba Donald Trump kan yadda take raunata hukumar CDC ta kasar Amurka, da hana ta taka rawa a kokarin dakile cutar COVID-19.

An ce, hukumar tamkar wani ginshiki ne ga aikin tabbatar da lafiyar jama'a a kasar Amurka, gami da a duniya baki daya. Amma duk da haka, wasu 'yan siyasar kasar na kokarin rage kudin da ake baiwa hukumar, lamarin da ya sa ta kasa daukar matakai masu dacewa wajen dakile yaduwar cutar COVID-19.

A karshen wannan sharhi ta ba da shawara cewa, a watan Janairun shekarar 2021, wani sabon shugaban kasar Amurka zai shiga White House, sai dai ya kamata wannan shugaba ya fahimta cewa, bai kamata ba a bar harkokin siyasa su haifar da tasiri ga aikin kiwon lafiyar jama'a.

Sa'an nan yayin da wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma ke tsamo wannan sharhin da mujallar "the Lancet" ta wallafa, ba su rufe kome ba sun yi bayanin cewa, "wata shahararriyar mujallar ilimin likitanci ta bukaci a maye gurbin shugaba Trump, gami da nuna goyon baya ga hukumar hana yaduwar cututtuka ta CDC ta kasarsa." (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China