Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rick Bright: Idan ba a maida hankali ba hunturun bana na iya zama mafi muni ga Amurka sakamakon sake bullar COVID-19
2020-05-15 10:10:53        cri
Kwararren masani a fannin binciken magunguna a Amurka, kuma jami'i a hukumar kiwon lafiyar kasar Rick Bright, ya ce idan ba a maida hankali wajen shirin tunkarar cutar numfashi ta COVID-19 dake iya sake bulla ba, lokacin hunturun bana na iya zama mafi muni a tarihi ga Amurka.

Rick Bright wanda ya yi wannan tsokaci gaban majalissar dokokin Amurka, bayan gabatar da takardar korafi a makon da ya gabata, ya ce damar da Amurka ke da ita na kankancewa. Kuma muddin mahukuntan kasar suka gaza daukar matakai bisa kimiyya, game da shawo kan annobar ta fannin samar da rigakafi, akwai yiwuwar cutar ta yi mummunar barkewa, kari kan cutar mura ta influenza da kan bulla a lokacin na hunturu.

Bright wanda a watan Afirilu, gwamnatin Amurka ta sallama daga mukamin daraktan cibiyar bunkasa nazarin kwayoyin halittu da magunguna ta kwararru ko BARDA a takaice, ya shaidawa 'yan majalissar kasar cewa, idan har ba a yi shiri sosai ba, lokacin sanyi na wannan shekara ta 2020, na iya zama mafi muni a fannin kiwon lafiyar Amurkawa.

Ya ce wajibi ne a baiwa masana kimiyya damar bayyana mahangar su ba tare da jin tsoron abun da ka je ya zo ba. Ya kuma yi kira da a daura damarar aiki tukuru, na samar da rigakafin cutar COVID-19 cikin watanni 12 zuwa 18 masu zuwa.

Jami'in dai ya rasa kujerarsa ne ta hukumar BARDA, bayan da a cewar sa, ya soki maganin da fadar gwamnatin Amurka ke yayatawa, a matsayin sahihin maganin cutar COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China