Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon firaministan Australia ya yi allah wadai da jita-jitar da kafofin watsa labarai dake karkashin jagoranci Rupert Murdoch ke yadawa kan cutar COVID-19
2020-05-09 17:09:00        cri

Jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya, ta wallafa sharhin tsohon firaministan kasar Australia, Kevin Michael Rudd a jiya, inda ya yi allah wadai da kafofin watsa labarai dake karkashin jagorancin Rupert Murdoch, dangane da jita-jitar da suka yada kan cutar numfashi ta COVID-19, domin taimakawa Donald Trump cimma nasara a babban zaben Amurka mai zuwa.

Cikin sharhin, Kevin Michael Rudd ya ce, a halin yanzu, ba a tabbatar da asalin cutar numfashi ta COVID-19 ba, amma kafofin watsa labarai dake karkashin jagorancin Rupert Murdoch na yada jita-jita game da cibiyar nazarin cututtuka ta birnin Wuhan, domin goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump, a babban zaben da za a yi.

A wannan mako, jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya ta ruwaito maganar wani dan leken asiri dake cewa, babu shaidun dake nuna cewa, cutar COVID-19 ta fito daga cibiyar nazarin cututtuka ta birnin Wuhan. Dan liken asalin ya kuma kara da cewa, jaridar The Daily Telegraph ta kasar Australia ta taba gabatar da wani rahoto mai shafuffuka 15, inda ta zargi kasar Sin da cewa, ta boye bayanan cutar numfashi ta COVID-19, amma ya ce, rahoton da ta gabatar ba shi da alaka da bayanan kawancen leken asiri ta Five Eyes Alliance. Haka kuma, jaridar The Daily Telegraph ta rubuta wannan rahoto ne bisa ra'ayoyin wasu mutane. Amma, jaridar The Guardian ta ruwaito maganar majiya dake cewa, rahoton ya samo asali ne daga Amurka, an kuma tsara wadannan labarai ne domin bata sunan kasar Sin, da matsa mata lamba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China