Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta hada kai da Canada kan samar da magunguna da rigakafin COVID-19
2020-05-13 20:09:16        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana tabbacin kasarsa na hada kai da kasashen duniya, ciki har da kasar Canada wajen samar da magunguna da rigakafin COVID-19.

Zhao Lijian ya bayyana haka ne Larabar nan, yayin taron manema labarai a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin,lokacin da yake karin haske kan rahotannin da kafafen yada labarai dake cewa, hukumar bincike ta kasar Canada ta bayyana jiya Talata cewa, Canada tana hada kai da kamfanin CanSino Bilogics na kasar Sin, a kokarin gwada alluran rigakafin da ake fatan samarwa nan gaba a kasar.

Ya ce, kwayar cuta ba ta san iyakar kasa ba, kuma kalubale ne dake addabar daukacin bil-Adama. Yana mai cewa, samun alluran rigakafi, yana da muhimmanci wajen kandagarki da hana yaduwar annoba, kuma shi ne kawai zai kai ga nasarar yakar COVID-19. Don haka, kasar Sin tana shiga alakar kasa da kasa da kasashen duniya, ciki har da kasar Canada wajen samar da magunguna da alluran rigakafin cutar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China