Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa cutar "taba ta lantarki" ta barke a bara a kasar Amurka?
2020-05-13 15:11:13        cri

Ya zuwa yau Laraba, bisa kididdigar da jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta yi, gaba daya mutane sama da miliyan 1.36 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, kana, mutane sama da dubu 80 sun rasu sanadiyyar wannan cuta.

Kuma abin da ya janyo hankulan jama'a shi ne, cutar "taba ta lantarki" ta barke a wuraren dake kusa da dakin gwajin halittu na Fort Detrick na rundunar sojan kasar Amurka, bayan da aka rufe dakin gwajin a watan Yuli na bara, kuma alamun kamuwa da cutar "taba ta lantarki" sun yi kama da na cutar numfashi ta COVID-19 sosai.

Mun san cewa, kasar Amurka ta fara sayar da taba ta lantarki daga shekarar 2007, amma me ya sa har zuwa bara, cutar "taba ta lantarki" take barkewa a kasar? Wannan tambaya ta sa Amurkawa, da al'ummun kasashen duniya, ke bukatar gwamnatin kasar Amurka, da ta yi bayani kan dangantakar dake tsakanin batun rufe dakin gwajin halittu na Fort Detrick da cutar "taba ta lantarki", da kuma dangatakar dake tsakanin cutar mura mai yaduwa da ta barke a kasar a bara da cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China