Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban Amurka ya fara takaita mu'amala da jama'a bayan kakakinsa ya kamu cutar da COVID-19
2020-05-11 10:36:03        cri

Wata kafar yada labarai a kasar Amurka, ta ce mataimakin shugaban kasar Mike Pence, ya fara nisantar jama'a bayan sakataren yada labaransa ya kamu da cutar COVID-19.

Devin O'malley, wani kakakin mataimakin shugaban kasar, ya ce Mike Pence zai yi amfani da shawarar da sashen kula da lafiya na fadar White House ya ba shi, kuma bai killace kansa ba. Yana mai cewa, gwaji ya nuna cewa mataimakin shugaban kasar bai kamu da cutar ba, kuma zai kasance a Fadar White House a yau Litinin.

Kafofin yada labarai na Associated Press da Bloomberg News sun yi amfani da kalamar 'kebe kai' domin bayyana matakan kariya da Mike Pence ya dauka, amma kafar yada labarai ta NBC ta ruwaito wani babban jami'i na cewa, babu batun kebe kai a cikin matakan kariya da ya dauka saboda babu wani abu da ya sauya daga cikin tsare-tsaren ayyukansa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China