Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta lashi takobin mayar da martani idan Amurka ta sanya sabon haraji kan kayayyakinta
2019-08-23 10:46:56        cri
Hukumar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar za ta mayar da martani, idan Amurka ta sanya karin haraji kan kayayyakinta.

Wannan na zuwa ne, bayan Amurka ta yi barazanar kara harajin kaso 10, kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 300.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce matsayar kasar Sin a bayyane take, wato, babu wanda zai amfana daga yakin cinikayya. Kuma kasar Sin ba ta kaunar yakin cinikayya, amma kuma ba ta tsoro, sannan za ta yi yaki idan akwai bukatar hakan.

Ya ce duk da cewa Amurka ta sanar da shirin dage sanya karin haraji kan wasu kayayyakin kasar Sin, duk wani sabon karin haraji daga Amurkar zai ta'azzara tankiyyar cinikayya.

Ya ce matakin karin haraji zai illata muradun Sin da Amurka, kuma mai yuwuwa, ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya.

Gao Feng yana fatan Amurka za ta dakatar da mummunar al'adar kakaba haraji, ta kuma cimma yarjejeniya da kasar Sin tare da samar da mafita ga matsalar, bisa adalci da mutunta juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China