Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Masar ya halarci taron Afrika ta bidiyo kan cutar COVID-19
2020-04-30 09:28:31        cri
A ranar Laraba shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya halarci kwarya-kwaryar taron kolin Afrika ta kafar bidiyo tare da sauran shugabannin kasashen Afrika da kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta shirya domin tattauna matakan hadin gwiwa kan yaki da annobar COVID-19 a nahiyar, fadar shugaban kasar Masar ne ta sanar da hakan.

Game da wannan batu, shugaban Masar ya jaddada muhimmancin tattaunawa a tsakanin kasashen Afirka domin hadin gwiwa da hada kai wajen aikin kawar da annobar ta COVID-19 daga nahiyar, kamar yadda kakakin shugaban kasar Masar Bassam Rady ya fada cikin sanarwar.

Cikin mahalarta taron na Afrika ta kafar bidiyo, ya hada da shugaban kungiyar AU na yanzu, kana shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, da shugabannin kasashen Kenya, Mali, Kongo DRC, Gabon, Nijer, Tanzania, Rwanda, Chad, Madagascar, da kuma firaministan Sudan.

Haka zalika taron ya samu halartar babban kwamishinan AU da daraktan cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afrika.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China