Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan kiwon lafiya na Afrika da Sin suna musayar kwarewa kan yaki da COVID-19
2020-04-30 09:45:59        cri
Kwararrun kiwon lafiya daga cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika wato Africa CDC, hukumar dake karkashin kungiyar AU, sun tattauna tare da takwarorinsu kwararrun kasar Sin game da muhimman hanyoyin da za'a koyi fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yaki da annobar COVID-19 don kawar da cutar daga nahiyar Afrika.

Wannan mataki na zuwa ne karkashin wani shirin hadin gwiwa na musamman game da yaki da cutar COVID-19 a fadin duniya wato GMCC a takaice, bisa koyi da nasarar da kasar Sin ta samu, an gudanar da taron ne a ranar Talata cikin hadin gwiwa tsakanin cibiyar Africa CDC da gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba.

Daraktan cibiyar Afrika CDC John Nkengasong, ya bayyana a taron hadin gwiwar na musamman don yaki da annobar cewa, nahiyar Afrika tana matukar godiya bisa ga tallafin da gidauniyar Jack Ma ke ci gaba da baiwa kasashen Afrika domin yaki da cutar COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China