Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Magajin garin Belleville a jihar New Jersey a Amurka ya ce ya kamu da cutar COVID-19 tun watan Nuwambar bara
2020-05-05 22:10:56        cri

 

Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar Amurka sun ce, magajin garin birnin Belleville dake jihar New Jersey ta kasar, Mista Michael Melham ya bayyana cewa, tun watan Nuwambar bara ya kamu da cutar mashako ta COVID-19. Kuma sakamakon gwajin baya-bayan nan da aka yi masa ya nuna cewa, yana dauke da kwayoyin halittar dake kare kansa daga harbuwa da wannan cuta. Bisa rahotannin da aka ruwaito a baya, an ce, an tabbatar da mutumin farko da ya kamu da cutar a karshen watan Janairun bana.

 

 

Mista Michael Melham ya ce, a watan Nuwambar bara, ya tafi birnin Atlantic City don halartar wani taro, amma bai ji dadi ba yayin da yake kan hanyar dawowa gida a ranar 21 ga watan. Da ya dawo gida, wasu alamun cutar sun fara bayyana a jikinsa, ciki har da zazzabi, da jin sanyi a jiki. Bayan da ya tuntubi likita, likitan ya yi hasashen cewa ya kamu da mura ne, kuma shi ma ya amince da wannan magana, saboda ba'a yi masa kowane irin gwaji ba.

 

 

Mista Michael Melham ya jaddada cewa, bai taba kamuwa da irin wannan mura mai tsanani ba a duk rayuwarsa. Har ma yana ganin cewa, akwai yiwuwar murar mai tsanani da mutane da dama suka kamu da ita a baya a Amurka, cutar COVID-19 ce, kuma akwai mutane da dama dake kusa da shi, wadanda su ma suka kamu da murar mai tsanani a watannin Nuwamba da Disambar bara. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China