Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya baiwa jihohi 12 na Amurka taimakon abin rufe baki da hanci miliyan 1.1
2020-05-06 10:45:09        cri

Kamfanin kera kayan gyaran motoci na Wanxiang na kasar Sin, mai hedkwata a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, ya ba jihohin Amurka 12 taimakon marufin hanci da baki sama da miliyan 1.1 da kuma marufin rufe fuska da ma'aikatan lafiya ke amfani da shi guda dubu 50, kuma tun a ranar Litinin da ta gabata, aka yi jigilar kashin farko na wadannan kayayyaki.

Kafin jigilar kayayyakin, tsohon gwamnan jihar Missouri Bob Holden ya bayyana godiya sosai ga karamin jakadan Sin dake Chicago Zhao Jian da kuma shugaban kamfanin Wanxiang reshen Amurka, Ni Pin ta kafar bidiyo, Zhao Jian da Ni Pin suna sa ido kan yadda aka yi jigilar wadannan kayayyaki.

Holden ya gaya wa Ni Pin cewa, matakin da kamfanin ya dauka ya farantar ran mutane da dama a Amurka, a cewarsa, wannan shi ne mu'amular al'adu tsakanin kasashen biyu, abun kuma dake da ma'ana matuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China