Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban janar Amurka: Ba mu san asalin kwayar cutar COVID 19 ba
2020-05-06 11:09:21        cri

Jiya Talata, a gun taron manema labarai da aka yi a Pentagon, game da tambayoyi ko an kirkiro wannan cuta daga dakin nazari na Wuhan ne? Ko cutar ta barke a kasuwar sayar da kayayyakin abinci na Wuhan ko sauran wurare, shugaban kungiyar hafsan-hafsoshin rundunar sojin kasar Amurka Mark Milley ya nuna cewa, ba mu san asalin kwayar cutar COVID-19 ba tukuna.

Ya ce, jama'a na mai da hankali sosai kan wannan batu, amma bisa binciken da aka yi, dimbin shaidu sun bayyana cewa, wannan cutar ta bulla ne daga indallahi, ba wani ya kirkiro ta ba.

Shugaban hukumar bincike annoba ta Amurka Anthony Fauci ya kuma shedawa manema labarai na National Geographic a Litinin da ya gabata cewa, nau'in kwayar cutar dake haddasa COVID-19 wato SARS-CoV-2 ba za a iya sarrafa ta ba ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China