Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
LOKACI YA YI DA ZA A DORA MUHIMMANCI KAN MAGUNGUNAN GARGAJIYA
2020-05-14 17:04:42        cri
Sanin kowa ne cewa, Bil Adama ya shafe tsawon zamani mai yawa yana amfani da magungunan gargajiya, domin warkar da kansa daga cututtuka dake addabarsa. Bahaushe kan ce "Jiki da Jini" salon magana da ke nuni da cewa, ba zai yiwu dan Adam ya rayu ba tare da fuskantar rashin lafiya sa'i sa'i ba. Don haka ne ma magunguna suka zama abokan hulda na dole ga al'umma, kamar yadda abinci ke zama jigon ci gaba da rayuwar mutum a duk inda yake a fadin duniyar nan.

Cikin kasashen duniya da suka shahara matuka wajen yin bincike da sarrafawa, da samar da magunguna gargajiya tun kafin fara sarrafa magunguna na Bature, ko na zamani, akwai kasar Sin dake gabashin duniya. Sin ta dade da amintuwa da nau'o'in magungunan gargajiya da take samarwa, wadanda suka hada da na sha, da na shafawa, da alluran magani da ake tsirawa a wasu sassan jiki, da tausa, da magani ta hanyar amfani da sassan wasu hallittu, tsirrai ko dabbobi. Dukkanin wadannan hanyoyi sun dade suna amfanar al'ummar Sinawa a tsawon dubban shekaru, tun kafin zuwa magungunan Bature cikin kasar ta Sin a karni na 19.

Tasirin irin wadannan magunguna ba zai misaltu ba, duba da cewa ko da a wannan gaba da kasar Sin ke yaki da cutar numfashi ta COVID-19, likitocin kasar Sin sun yi amfani da nau'o'in magungunan gargajiya daban daban, domin jinyar masu dake da cutar.

Idan kuma mun lura da cewa magungunan gargajiyar Sin sun shafe tsawon dubban shekaru ana amfani da su, ke nan ko shakka babu, amfanin su ne ya sanya su karbuwa da shafe zamani mai yawa ana damawa da su.

Baya ga kasar Sin, kasashen duniya da dama ciki hadda kasashen nahiyar Afirka, su ma sun shafe tsawon lokaci suna amfani da nau'o'in magungunan gargajiya masu amfani matuka. Ko da yake a Afirka, da yawa daga irin wadannan magunguna ba sa samun damar zuwa dakunan bincike, ko gwajin kimiyya, ko ma amincewa daga sashen kiwon lafiya, sabanin yadda abun yake a kasar Sin.

To ko da wace mahanga muka kalli magungunan gargajiya dai, muna iya shaida cewa, sun yi matukar taka rawa wajen ba da jiyya ga al'ummun sassan duniya da dama a tsawon shekaru, kuma da yawa daga cikinsu, musamman wadanda ake samarwa daga tsirrai, ba sa dauke da sinadarai masu illata lafiyar al'umma. Kari kan hakan, suna kuma samarwa al'ummun kasashen da suke sarrafa su guraben ayyukan yi, da rage yawan kudaden musaya na cinikayyar magungunan yammacin duniya da ake safarar su.

A baya bayan nan, shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina, ya gabatar da wani nau'in maganin gargajiya na sha, wanda ya ce yana maganin cutar numfashi ta COVID-19, cutar da kawo yanzu ta shafi kusan dukkanin sassan duniya, inda ta harbi adadin mutanen da yawan su ya kai miliyan 4 da 'yan kai, kana ta hallaka mutane da yawan su ya haura 240,000.

A cewar shugaba Rajoelina, maganin da kasar sa ta samar mai suna CVO a takaice, wata nasara ce ga nahiyar Afirka, musamman fannin cin gajiya daga magungunan gargajiya. To sai dai kuma a bangare guda, masu ruwa da tsaki daga sassa daban daban na kiwon lafiya, ciki hadda hukumar lafiya ta duniya WHO, na nuna shakku kan ingancin maganin na Madagascar, duba da cewa maganin bai samu gwaje gwajen masana kafin amincewa da shi ba.

A baya ma dai an sarrafa wani magani na magance cutar zazzabin cizon sauro da sinadaran tsiron "Artemisia annua", wanda a wannan karon ma shi ne Madagascar ta yi amfani da shi wajen sarrafa maganin CVO. Tuni kuma kasar ta gabatar da maganin kyauta ga wasu kasashen Afirka, ciki hadda janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Guinea-Bissau, da Equatorial Guinea, da Liberia, da Tanzania da Najeriya da janhuriyar Nijar da dai sauran su.

A halin da ake ciki yanzu haka, da duniya ke fuskantar matsananciyar bukatar maganin kandagarki, da yaki da cutar COVID-19, lokaci ne mafi dacewa da ya kamata masu binciken kimiyya, da masana fannin kiwon lafiya, su kara maida hankali matuka ga ingancin magungunan gargajiya, kasancewar su masu saurin samuwa, sama da magungunan zamani da a kan dauki lokaci mai tsawo ana bincike, da gwajin su kafin Bil Adama ya ci gajiyar su. Baya ga kuma lokaci mai tsawo da ake shafewa ana gwajin su, domin kaucewa illar da sinadaran dake cikin su ka iya yiwa masu amfani da su a kusa ko a nesa.

A jimlace dai ana iya cewa, akwai bukatar kara dora muhimmanci kan binciken managartan magungunan gargajiya, wadanda za su iya tallafawa fannin kiwon lafiyar al'ummar duniya, saboda dalilai masu yawa, kamar samar da zabi ga masu bukatar amfani da nau'o'in magunguna daban daban, da batun kaucewa amfani da magunguna masu haifar da illa ga jikin bil Adama, da samar da karin guraben ayyukan yi ga masu fasahar samar da magunguna, musamman a kasashe masu tasowa, da kuma kare darajar fasahohin al'ummun duniya da ake gada daga kaka da kakanni.

Bugu da kari bunkasa samarwa, da inganta magungunan gargajiya, ba da damar shigar sassan duniya da ke a sahun baya yanzu, cikin kasuwar magunguna ta duniya a nan gaba, ta yadda za su yi takara tare da cimma moriya tare da sauran sassa masu karfi da tasiri a wannan fanni. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China