Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta alkawarta karfafa tasirin manyan dokoki don daidaita ginshikan tattalin arzikinta
2020-05-14 10:46:37        cri
Zaman majalissar zartaswa na Sin na jiya Laraba, ya ce kasar za ta karfafa tasirin manyan dokokinta, don daidaita ginshikan tattalin arziki. Kaza lika kasar za ta hade sassan manufofin kudi da na hada hadar kudi, da inshorar al'umma, da fannin bunkasa ayyukan yi, manufofin da ko shakka babu, za su karfafa manyan bukatun ci gaba da daidaito a bangarori guda 6.

Rahotanni sun nuna cewa, taron wanda firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, ya yi kira da a kara azama wajen tabbatar da nasarar wadannan muhimman bukatu guda 6. Bangarorin dai sun kunshi samar da guraben ayyukan yi, da kyautata rayuwar jama'a, da bunkasa kasuwa, da samar da isasshen abinci da makamashi. Sauran su ne daidaita ayyukan masana'antu, da fannin samar da kayayyaki, da kuma inganta harkokin gudanarwa a mataki na al'umma.

Taron ya yi amannar cewa, wadannan muhimman bukatu 6, kasar za ta samu zarafin daidaita muhimman bangarori guda 6. Bangarorin sun hada da na daidaita guraben ayyukan yi, da na kudi, da cinikayyar waje, da fannnin zuba jarin waje. Sai kuma zuba jari a cikin gida, da hasashen ribar kasuwanni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China