Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda za a bayyana raguwar tattalin arzikin Sin na 6.8% a rubu'in farko na bana
2020-04-20 14:15:37        cri
Tattalin arzikin kasar Sin ya ragu da 6.8% a rubu'in farko na bana, adadin mafi kasa tun lokacin da aka fara gabatar da bayanan rubu'i-rubu'i na alkaluman GDPn kasar daga shekarar 1992.

Amma, bangarorin tattalin arziki na kasar Sin da ma hukumomin tattalin arzikin kasashen ketare ba su nuna damuwa sosai ba kan wannan adadi, sabo da wannan raguwa na gajeran lokaci ne kawai. A tsakiyar watan Maris, kimanin kaso 99 cikin 100 na kamfanoni da masana'antu sun dawo bakin aiki, haka kuma manyan kasuwannin kasar Sin, da tsarin masana'antu mai inganci, da tarin ma'aikatan kwadago da tsarin samar da kayayyaki mai karfi dukkansu sun tabbatar da tushen tattalin arziki mai inganci da ci gaba na tattalin arziki a nan gaba.

Binciken nazarin kan tattalin arzikin kasar Sin, na nuna cewa, raguwar tattalin arzikin kasar Sin mafi muni ta riga ta wuce. Tattalin arziki da zaman takewar al'umma na ci gaba da farfadowa daya bayan daya, kana wasu manyan alkaluman tattalin arziki sun nuna alamun ci gaba da karuwa. Sabon hasashen da kamfanin Morgan Stanley na kasar Amurka ya yi, ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai karu da 1.5% a rubu'in biyu na bana, kana, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zai karu da 1.2 % a bana, wadda za ta kasance daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki kalilan da za su samu karuwar tattalin arziki a bana.

Haka kuma, kasar Sin tana ci gaba da samar da wasu labaru masu kyau, kamar gabatar da karin manufofin yin rangwame, wadanda za su samar da tasiri mai kyau ta fuskar bunkasa tattalin arziki. Hasashen da IMF ya yi, ya nuna cewa, mai iyuwa ne, tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kaso 9.2% a shekarar 2021. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China