Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana'antun kasar Sin mallakar gwamnatin kasa sun zuba RMB biliyan 3.2 wajen yaki da kangin talauci
2020-03-17 13:10:40        cri

Wakilinmu ya samu labari daga kwamitin kula da kadarorin gwamnati na majalisar gudanawar kasar Sin a kwanan baya cewa, a shekarar 2020 da muke ciki, komai wahalar da za su fuskanta wajen tafiyar da harkokinsu sakamakon barkewar annoba, masana'antun kasar mallakar gwamnatin tsakiya sun yi alkawarin zuba kudin Sin RMB miliyan 3201, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 458 kyauta, ga gundumomi guda 246 masu fama da talauci, adadin da ya karu da yuan miliyan 692 bisa shekarar bara.

Rahotannin sun nuna cewa, tun daga shekarar 2015 har zuwa yanzu, masana'antun kasar mallakar gwamnatin tsakiya sun zuba da kuma shigar da taimakon kudi da yawansu ya kai yuan biliyan 20.6 baki daya, kudaden da suka kara azama kan samun saurin ci gaban wuraren masu fama da talauci, da kuma kara kudin shigar masu fama da talauci. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China