Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Sin: Annobar COVID-19 ba za ta canza yanayin ciniki na dogon lokaci ba
2020-02-24 19:55:30        cri
Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, Ren Hongbin, ya furta a yau Litinin cewa, annobar cutar COVID-19 ba za ta canza nagartaccen yanayin da ake ciki a kasar Sin, a fannin ciniki da kasashen waje, cikin dogon lokaci mai zuwa ba. Sa'an nan cutar ba ta raunana karfin kasar ta fuskar janyo jari daga ketare ba, kasancewar Sin za ta ci gaba da zama kasar da ake son zubawa jari.

Jami'in ya yi furucin ne, yayin wani taron manema labaru na ofishin watsa labarun majalisar zartaswar kasar Sin, inda ya ce don taimakawa kamfanonin kasar su maido da ayyukansu na samar da kayayyaki, a lokacin da ake fama da annobar, ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta gabatar da wasu manufofi guda 20, don tabbatar da ingancin ciniki da kasashen ketare, da janyo jarin waje, gami da fannin sayen kayayyaki.

A nasu bangare kuwa, hukumomi masu kula da kudi, da haraji, da babban bankin kolin kasar, da hukumar kwastam, dukkansu suka dauki wasu matakai na tallafawa kamfanoni.

Jami'in ya kara da cewa, matakan da ma'aikatar kasuwanci za ta dauka, sun hada da taimakawa kamfanoni masu jarin kasashen waje su farfado da ayyukansu, da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla da kamfanonin kasashen waje masu alaka da wasu manyan ayyuka, da kara bude kofa ga jarin waje, domin su shiga cikin karin sana'o'i, da karfafa ayyukan kare hakkin kamfanoni masu jarin waje, don kyautata muhallin zuba jari ga 'yan kasuwan kasashen waje, ta yadda za su samu karin imani wajen zuba jari, da gudanar da harkokinsu a kasar Sin cikin dogon lokaci mai zuwa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China