Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman tattalin arzikin Sin na ci gaba da kyautatuwa a watan Maris
2020-04-20 17:21:26        cri
Bisa labarin da aka samu daga kwamitin kwaskwarima da raya kasa na Sin a yau Litinin, an ce, a watan Maris, alkaluman tattalin arzikin kasar Sin suna ci gaba da karuwa, yanayin tattalin arzikin kasar yana farfadowa. Kuma sha'awar zuba jari da kamfanonin kasashen Amurka da Japan dake kasar Sin suka nuna a watan Maris ya karu, idan an kwatanta da watan Fabrairu.

A taron manema labaran da aka yi a yau, kakakin kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin Yuan Da, ya bayyana cewa, kamfanoni masu jarin waje dake kasar Sin suna gaggawar dawowa bakin aiki, sakamakon nasarar da aka cimma wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Kuma hukumomin da abin ya shafa za su ci gaba da maida hankali kan gudanar da manyan shirye-shirye masu jarin waje. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China