Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu alama mai armashi a kasuwannin sayayya na kasar Sin
2020-03-06 13:18:49        cri
Wang Bin, mataimakin shugaban sashen tafiyar da harkokin kasuwanni na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana jiya a nan Beijing cewa, a kwanakin baya, an samu alama mai armashi a kasuwannin sayayya na kasar Sin, inda aka farfado da sayar da kayayyaki.

Wang ya yi bayanin cewa, manyan dalilai 3 da suka sa aka farfado da sayar da kayayyaki su ne, da farko, an yi kandagarki da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar yadda ya kamata. Na biyu kuma masana'antu sun gaggauta komawa bakin aiki, kuma haka lamarin yake a wajen ma'aikata, kana ana farfado da ayyuka da zaman rayuwa yadda ya kamata cikin hanzari. Na uku kuwa, mutane sun fara sayayya kamar yadda suka saba yi a baya. Wang Bin, ya yi hasashen cewa, za a ci gaba da farfado da sayar da kayayyaki a kasar sakamakon kara dakile yaduwar annobar da kuma maido da ayyuka da zaman rayuwa kamar yadda suke a baya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China