Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sanda: An kashe mutane 4 a wani hari a tsakiyar Najeriya
2020-05-14 10:45:31        cri
Hukumar 'yan sanda a jahar Benue dake shiyyar tsakiyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu mutanen kauye 4 da kuma jikkata mutane 3 bayan wani hari da 'yan bindiga suka kaddamar.

Hukumar 'yan sandan jahar ta tabbatar da cewa, a ranar Talata wasu mahara kan babura suka kai hari kauyen Tse-Haaga dake karamar hukumar Guma a Benue.

Mutane biyu sun mutu a harin. Daga bisani biyu daga cikin mutanen da aka raunata suka rasu yayin da ake kokarin kai su asibiti, kakakin 'yan sandan jahar Benue, Catherine Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin ga 'yan jaridu.

Ana cigaba da gudanar da bincike kan musabbabin harin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China