Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin kasar Sin ya samar da cibiyar kula da masu COVID-19 mai gadaje 300 a Nijeriya
2020-05-13 10:51:26        cri

Kamfanin gine gine na kasar Sin dake aiki a Nijeriya, ya bada gudunmuwar cibiyar kula da masu cutar COVID-19, mai gadaje 300 ga kasar.

Cibiyar gudunmuwa ce daga abokan hulda na bangarori masu zaman kansu, ciki har da kamfanin gine-gine na CCECC, domin dakile yaduwar COVID-19 a Nijeriya.

Kamfanin na CCECC ya ce gudunmuwar cibiyar muhimmin kari ne kan kayayyakin kiwon lafiya da Nijeriya ke da su, a yayin da take yaki da cutar COVID-19.

Kamfanin ya kuma samar da naurorin taimakon numfashi 2 da na samar da iskar shaka guda 1 da kuma marufin baki da hanci 10,000 .

Ana sa ran sabuwar cibiyar mai dauke da dukkan kayayyakin jinya ya zama kari kan cibiya mai dauke da kusan gadaje 1,000 da Abuja, babban birnin kasar ke da su wajen kebewa da jinyar masu cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China