Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya na fatan nada Joseph Yobo matsayin kocin Super Eagles
2020-05-12 10:09:52        cri
Hukumar kwallon kafar Najeriya, ta fara aiwatar da wasu matakai na baiwa tsohon dan wasan babbar kungiyar kwallon kafar kasar wato Super Eagles Joseph Yobo, damar jagorantar kulaf din a nan gaba.

A watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar ta NFF, ta nada Joseph Yobo a matsayin mamban tawagar kwararru, kuma mataimakin kocin kungiyar ta Super Eagles, wanda hakan daya ne daga matakan da ake dauka domin daga matsayin sa a tawagar.

Wannan ne karon farko da wani tsohon dan wasan kungiyar ya samu damar darewa wannan babban mukami a Super Eagles

Da yake tabbatar da wannan aniya yayin zantawarsa da manema labarai a jiya Litinin, shugaban hukumar NFF Amaju Pinnick, ya ce suna fatan nan gana Yobo zai kasance babban kocin Super Eagles, kuma hakan ne ya sa aka sanya shi cikin tawagar kwararru ta Super Eagles, kafin nan gaba a nada shi babban kocin kungiyar.

Bugu da kari a cewar Mr, Pinnick kasancewar Yobo tare da tawagar Super Eagles zai taimaka matuka, duba da cewa zai tallafa wajen kara gina tawagar, wadda za ta buga gasar cin kofin Afirka dake tafe a shekarar 2021, da kuma wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022.

A baya dai Yobo ya rike mukamin kyaftin din Super Eagles, ya kuma halarci gasar cin kofin duniya sau 3 tare da kungiyar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China