![]() |
|
2020-05-12 09:39:39 cri |
Saeed Sambo, shugaban karamar hukumar Gwoza dake jahar, ya ce mayakan 'yan ta'addan da dama sun tsere daga yankin a ranar Lahadi a lokacin fafatawar.
Sambo ya fadawa 'yan jaridu cewa dakarun sojojin sun yi musu rakiya a lokacin da mayakan na Boko Haram suka yi musu kwanton bauna a garin.
Jami'in ya kara da cewa, mayakan sun kaddamar da hare hare masu yawa ta hanyar amfani da ababen fashewa da suke amfani dasu daga bisani suka yi harbe harbe. Sai dai kuma, dakarun sojojin sun mayar musu da martani mai tsanani.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China