Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 17 a yaki da ta'addanci
2020-05-12 10:13:50        cri
An kashe 'yan bindiga 17 yayin aikin sintiri na yaki da ta'addanci wanda sojojin Najeriya suka kaddamar a jahar Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, rundunar sojojin Najeriya ce ta tabbatar da hakan a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, da dama daga cikin mayakan sun tsere, dauke da raunukan harbin bindiga a jikinsu, bayan da sojojin suka bude musu wuta a yankin Gwagwada dake karamar hukumar Chikun a jahar Kaduna a ranar 7 ga watan Mayu.

Aikin yaki da ta'addancin wani bangare ne daga cikin shirin musamman da sojojin Najeriyar suke gudanarwar da nufin kakkabe 'yan ta'adda da masu aikita muggan laifuka a arewacin kasar.

Sojojin sun yi nasarar tarwatsa manyan mafakar 'yan bindigar uku a kauyukan Mashigi Galbi, Damba, da Kabarasha, a jahar Kaduna, a cewar sanarwar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China