Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD:Sama da mutane miliyan 1.3 ambaliyar ruwa ta shafa a gabashin Afrika
2020-05-13 10:56:58        cri

Ofishin kula da agajin jin kai na MDD, ya ce akalla mutane miliyan 1.3 ambaliyar ruwa ta shafa, sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi tun cikin watan Maris, a yankin gabashin Afrika.

Ofishin ya ce alkaluman sun hada da akalla mutane 481,000 da suka rasa matsugunansu a kasashen Burundi da Djibouti da Habasha da Kenya.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi kamari a yankuna masu yawa na gabashin Afrika a makonnin baya bayan nan, wanda ya haddasa asarar rayuka da rashin matsuguni da ambaliya da zaftarewar kasa da lalata gidaje da kayayyaki da rayuwar jama'a.

A cewar kungiyar raya gabashin Afrika (IGAD), galibin tasoshin hasashen yanayi na yankin sun bada rahoton samun ruwan sama mafi yawa da ba a gani ba cikin kusan shekaru 40.

Ofishin na MDD ya ce, baya ga tasirinsa kan iyalai da al'ummomi, ruwan saman mai karfi a yankin, ya samar da yanayi mai kyau na kara hayayyafar farin dango. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China