Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika na godiya ga taimakon da Sin take ba su
2020-04-22 14:40:34        cri

Jirgin saman dake sufurin kayayyakin tallafi da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa demokuradiyyar Kongo don taimaka mata wajen yakar cutar COVID 19, ya isa birnin Brazzaville, fadar mulkin kasar a ran 15 ga wata, bisa agogon wurin. Ministan harkokin wajen kasar Jean-Claude Gackosso ne ya tarbi wadannan kayayyaki inda ya ce, ba za a iya ganin sahihiyar abokiyar kasar ba sai tana cikin mawuyacin hali. A cewarsa, har ila yau akwai dalibai 'yan kasar fiye da dubu 1 dake karatu a kasar Sin, kuma gwamnatin kasar Sin na ba su kulawa sosai.

Ban da wannan kuma, ministar lafiya ta kasar Jacqueline Lydia Mikolo ta nuna cewa, yauzu kasar na matukar karancin kayayyakin kandagarkin annobar, taimakon da Sin ta samar mata na zuwa kan lokaci. Kuma wadannan kayayyaki na da inganci matuka.

Gidan telibijin na kasar VOX ya da labari cewa, wannan ba shi ne karo na farko kuma ba karo na karshe ba da Sin take baiwa kasashen Afrika taimako wajen yakar cutar.

An ce, dimbin kayayyakin tallafi da Sin ta baiwa kasashen Afrika 18 sun isa Ghana a ran 6 ga wata, don a yi sufurinsu daga Ghana zuwa kasashen Najeriya da Senegal da kuma Gabon, da Saliyo da Guinea Bissau, sannan da Guinea da kuma Cote D'ivoire da Gambia, kana da Laberiya da Mali da kuma Burkina Faso, har da Equatorial Guinea, da Togo da Benin da demokuradiyyar Kongo, da Cape Verd, da Sao Tome and Principe da dai sauran kasashe 17 dake tsakiya da yammacin Afrika. Ta hanyar samar da tallafin jin kai ta hannun MDD, wadannan kayayyaki za su taimakawa kasashen tinkarar mawuyacin hali na matukar bukatar kayayyakin kandagarki.

 

 

Ban da samar da kayayyakin tallafi, gwamnatin kasar Sin ta turawa kasashen Habasha da Burkina Faso tawagar jami'an lafiya a ranar 16 ga wata don taimaka musu yakar cutar.

 

 

Sin da Afrika sun kulla dangantakarsu lokacin da suke cikin mawuyacin hali, ba wanda zai hana bunkasuwar zumuncin bangarorin biyu duk da cewa akwai wasu masu yunkurin illata shi. Shugaban hukumar AU ya nuna cewa, Afrika da Sin abokan juna ne dake tinkarar abokan gaba tare, kuma suna da makoma iri daya masu alaka da juna matuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China