Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Zaman kulle na wata daya a Afirka ya haifar da hasarar dala biliyan 65.7
2020-05-11 10:18:15        cri
Wani rahoto da hukumar MDD mai lura da tattalin arzikin Afirka ko ECA ta fitar a jiya Lahadi, ya nuna cewa matakin kulle da kasashen Afirka da dama ke aiwatarwa domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, a wata guda kawai, ya haifarwa nahiyar asarar dalar Amurka biliyan biliyan 65.7, adadin da ya kai kaso kusan 2.5 bisa dari na GDPn nahiyar na shekara baki daya.

Sabon rahoton mai taken "COVID-19: Dabarun fita daga kulle na Afirka," ya kuma bayyana cewa akalla kasashen nahiyar 42 ne suka aiwatar da dokar kulle ta baki daya, ko kuma wani bangare na dokar, a wani yunkuri na dakile yaduwar wannan annoba. A hannun guda, ya gabatarwa kasashen na Afirka wasu dabaru na fita daga yanayin na kulle, sakamakon illar da matakin ke yiwa tattalin arzikinsu.

Cikin dabaru 7 da hukumar ta ECA ta gabatar hadda samar da yanayi mai dorewa, da rage radadi, da farfado da harkokin tattalin arziki. Rahoton ya gabatarwa nahiyar wasu dabaru da tuni aka gwada aiwatar da su a wasu yankuna na duniya, ya kuma fayyace irin hadarinsu ga Afirka. ECA ta kuma tabbatar da cewa, batu mafi sarkakiya ga masu tsara dokokin nahiyar shi ne, tasirin kulle sakamakon COVID-19 ga samuwar abinci.

A jiya Lahadi, cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta Afirka, ko Africa CDC, ta ce ya zuwa yammacin ranar, yawan al'ummar nahiyar da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 a sassan Afirka ya haura mutum 61,165, yayin da tuni cutar ta hallaka mutum 2,239. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China