Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu mutuwar karin mutane 13 dake da alaka da COVID-19 a Afrika ta kudu
2020-05-02 17:04:23        cri
Afrika ta kudu ta bada rahoton samun sabbin mutane 304 da suka kamu da COVID-19 da wasu 13 da suka mutu sanadiyyar cutar, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu sanadin cutar zuwa 116.

Ministan lafiya na kasar Zweli Mkhize, ya bayyana a jiya cewa, an samu sabbin mace-macen ne a lardunan yammacin da gabashin Cape da Guateng da KwaZulu Natal.

Ya ce la'akari da matakin da suka dauka na bada rahoton mace-macen da kadai aka tabbatar, akwai jinkiri wajen tantancewa da tabbatar da wasu daga cikin rahotannin.

Ya zuwa jiya Juma'a, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 5,951, yayin da 2,382 suka warke a kasar Afrika ta kudu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China