Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ECA: yankin cinikayya maras shinge na Afirka na iya tallafawa nahiyar sake farfadowa
2020-05-13 10:34:59        cri

Darakta mai kula da dunkulewar yankuna da cinikayya, a hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta ECA, Mr. Stephen Karingi, ya ce yankin cinikayya maras shinge na Afirka, na iya tallafawa nahiyar wajen sake farfado da tattalin arzikin ta, wanda cutar numfashi ta COVID-19 ta yiwa mummunan tasiri.

Karingi wanda ya zanta da manema labarai ta bidiyo a ranar Litinin, ya ce idan da nahiyar ta aiwatar da yarjeniyoyi kamar na gudanar da cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasashen Afirka ko AfCFTA a takaice, da hakan ya haifarwa nahiyar dama ta fadada, da karfafa hada hadar kasuwanci, ta yadda hakan zai rage tasirin da COVID-19 din ke yiwa nahiyar.

Jami'in ya kara da cewa, sauran dabarun da ka iya taimakawa nahiyar, sun hada da na raya fannin sarrafa magunguna, da inganta fannin noma da raya masana'antu. Kaza lika a cewar sa, bunkasa hada hadar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar, shi ma mataki ne na samar da karin guraben ayyukan yi, da kudaden musaya, da bunkasa masana'antu, da gina tattalin arzikin nahiyar.

Daga nan sai ya yi nuni da irin yadda bullar cutar COVID-19 ya haskaka muhimmancin rungumar amfani da fasahohin zamani ta fuskar kasuwanci, yana mai cewa, kamata ya yi kasashe mambobin ECA, su dora muhimmanci kan dabarun aiwatar da harkokin cinikayya ta amfani da fasahohin sadarwa, matakin da ke da alaka ta kusa, da mataki na 2 na aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China