Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 46,000 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika
2020-05-05 11:30:50        cri

Jimilar mutane 46840 ne aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, yayin da 1835 suka mutu, ya zuwa jiya Litinin a nahiyar Afrika.

A yanzu, kasashe 7 na da mutane sama da 2,000 da aka tabbatar sun kamu, ko kuma kimanin 2/3 jimilar mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar. Kasar Afrika ta kudu na da mutane 7,220 da aka tabbatar sun harbu, sai Masar dake da mutum 6,813, Morocco na da 5,053, Algeria na da mutum 4,648, sai Ghana dake da mutane 2,719, Nijeriya na da mutane 2,558 sai kuma Kamaru dake da mutane 2,077 da suka harbu.

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce adadin masu kamuwa da cutar a kasar ka iya karuwa cikin sauri a watanni masu zuwa.

Yayin wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasarsa a daren jiya, shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya sanar da tsawaita matakin kulle na makonni 5, da karin kwanaki 14.

Shi kuwa Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio, ya sanar da kammala kebe kansa na tsawon kwanaki 15, bayan gwaji ya nuna baya dauke da cutar. Ana sa ran Shugaba Bio ya koma aiki gobe, 6 ga wata, yayin da kasar ke shiga kwana na 3 karkashin matakin kulle da ya fara aiki a ranar 3 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China